A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, lokacin ƙuruciya shi ne mafi dacewa wajen shuka ƙwayar sani da kyawawan ɗabi’u a cikin ruhin yaro. Ba da labaran annabawa da Ahlul Baiti daga iyaye yana da tasiri mai ɗorewa a cikin zuciyar yaro. Marigayi Ayatullah Ha’iri Shirazi ya ɗauki wannan hanyar tarbiyya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan da iyaye za su yi.
Ayatullah Ha’iri Shirazi (Allah Ya jikansa) Yace: "Na tuna lokacin da nake yaro, idan kowa a gida ya yi barci, a ƙarshen dare nakan zo wajen mahaifina. A lokacin yarintata, ya kasance yana ba ni labaran annabawa a wani lokaci, labari guda yakan ɗauki darare da dama, kuma ni ma ina daurewa ina saurara.
Duk lokacin da ba da labari ya zo daidai da kwanakin Muharram, mahaifina ya kasance yana ba da labarin abin da ya faru a Ashura da tafiyar Imam Husaini, da yadda aka nemi ya yi mubaya’a ga Yazidu a Madina, da sauran abubuwan da suka faru, dalla-dalla kuma dare bayan dare.
Waɗannan abubuwa suna da tasiri sosai. Wato, ɗaya daga cikin manyan ayyukan da uba da uwa za su yi wa ɗansu shi ne su ba yaro tarihin waɗannan mutane. Wannan yana yin tasiri a cikin halayen yaro tun daga yarintarsa. Yana yin tasiri a cikin ɗabi’unsa, ayyukansa, halayensa, ibadarsa, sallarsa da azuminsa, kuma duk waɗannan abubuwa suna gyaruwa.
Madogara: Ofishin Kiyayewa da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Ha’iri Shirazi (Allah Ya jikansa)
Ra'ayinka